Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudancin Najeriya Ya Dage Kan A Sakewa Kasar Fasali


Wasu 'yan kudancin Najeriya
Wasu 'yan kudancin Najeriya

A jawabin da shugaban Najeriya ya yiwa kasar majalisun dokokin tarayya da na zartaswa ke da alhakin tattaunawa akan makomar Najeriya abun da bai yiwa wasu shugabannin kudancin kasar dadi ba da yanzu suka dage sai an sakewa kasar fasali.

Shugaban ya bayyana cewa majalisun dokokin tarayya da na zartsawa ne kadai suke da hakin tattaunawa akan makomar Najeriya bisa ga kundun tsarin mulkin kasar da ma dokokinta.

Kalaman na Shugaba Buhari ba su yiwa wasu 'yan Najeriya dadi ba musamman kungiyoyin kare hakin bil Adama da na masu fafutika da suka fito daga kudancin kasar.

A taron manema labarai da suka kira a Legas kungiyoyi da dama da suka hada da NADECO, da Afenifere, kungiyar Yarbawa zalla sun bayyana rashin amincewarsu da kalaman shugaban kasa saboda inji shugaba Buhari batun tattaunawa akan makomar kasar ba abu ne da za'a dinga cecekuce a kai ba.

A cewar kakakin kungiyar Afenifere Mr. Yinka Odumakin matsayinsu shi ne a ga anfara tattaunawa akan makomar Najeriya musamman idan aka yi la'akari da halin da kasar ta shiga lamarin da yanzu ya zama tamkar babu yadda tsakanin al'ummomin kasar.

Odumakin na mai cewa ganin yadda kungiyoyi daban daban ke kira ga gwamnati ta soma tattaunawa kan yadda za'a sake fasalta Najeriya,wajibi ne gwamnati ba bar al'ummar kasar su soma duba matsalolin da suka addabi kasar.

Ta bakin Odumakin sun shawarci shugaban kasa da ya sani cewa Najeriya na cikin wani hali na kakanikayi kuma tana neman shugaba jarumi da zai tsaya ya ga an fitar da kasar daga halin da take ciki yanzu. Lokaci yayi da za'a sake fasalta Najeriya, a sata kan sabon turban da zai sa ta cigaba, inji Odumakin.

Sai dai kudancin Najeriya din na zargin cewa arewacin kasar ba ta son a sakewa kasar fasali saboda 'yan arewacin kasar ke cin moriyar salon tafiyar ta yanzu.

Alhaji Ado Dansudu wani shugaban kungiyar 'yan arewacin Najeriya dake Legas yana mai cewa wata dabara ce ta raba kasar. Yanzu Najeriya ba ta kai lokacin da za'a sake fasalinta ba saboda kasar tana cike da kabilanci da banbancin addini.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG