Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudin Dake Asusun Ajiya Na Kasar China Zai Kare A Shekarar 2035


Rahotanni a baya-bayan nan na cewa, kudin dake asusun ajiya na kasar China zai kare a shekara ta 2035, wannan ya janyo cece kuce a hanyar sadarwa ta Internet.

Wasu ‘yan kasar China sun yi ikirarin cewa masu ritaya suna karbar fansho mai tsoka a kowane wata yayin da wasu suke nuna damuwa akan cewa asusun kudin zai kare kafin su yi ritaya.

Masana Tattalin arziki sun ce an yi gyare-gyare na gaggawa don magance matsalar masu kabar kudin fansho a kasar ta China, amma duk da haka suna ganin cewa tattalin arzikin zai kara tsananta da yawan mutanen da ke tsufa, da kuma raguwar ma'aikata da raguwar haihuwa.

Asusun ajiyar kudi na kauyuka na kasar China, shine kashin baya na tsarin fansho na kasar, ya samu kudin Yuan 4.8 trillion (dala Amurka biliyan 714) a karshen shekara ta 2018, ko kuma kashi 5.3 bisa dari na yawan kayan da ake sarrafawa a cikin gida, kamar yadda rahotanni suka nuna a Kwanan nan na Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Jama'a ta kasar China mai tallafa wa gwamnati.

An yi kiyasin cewa, asusun da aka kafa a shekarar alif dari tara da casa’in da bakwai (1997), zai kai kusan yuan trillion 6.99 a shekarar 2027, kafin a hankali ya rika raguwa har ya kare kafin shekarar 2035, bisa ga cewar kwararrun jami'an gwamnati.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG