Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudirin Sauyin Haraji Ya Tsallake Karatu Na 2


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ba a tsara kudurorin domin wani yanki ba sai dai don a bunkasa Najeriya baki daya.

A yau Alhamis Majalisar Dattawan Najeriya ta zartar da kudurorin haraji guda 4 da suka samu tsallakawa zuwa karatu na 2 ta hanyar kada kuri’ar murya.

A ranar 3 ga watan Oktoban da ya gabata Shugaba Bola Tinubu ya aikewa Majalisar Dokokin Najeriya da kudurorin sauye-sauyen haraji guda 4.

Matakin ya janyo cece-kuce inda gwamnonin jihohin arewa ke adawa da sauye-sauyen harajin.

Sakamakon damuwa da halin da ake ciki, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ba a tsara kudurorin domin wani yanki ba sai dai don a bunkasa Najeriya baki daya.

Majalisar Dattawa ta kuma zartar da kudirin kafa hadaddiyar hukumar haraji da kotun daukaka kara a kan haraji da hukumar karbar korafi da binciken laifuffukan haraji domin karatu na 2, a matsayin wani bangare na kunshin sauye-sauyen harajin gwamnatin Tinubu.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG