Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kun San Dalilin Da Ya Sa Limamin Masallacin Makka Ya Ziyarci Gwamna Zulum?

Daya daga cikin Limaman Masallacin Makka, Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari (Twitter/ @GovBorno)
Daya daga cikin Limaman Masallacin Makka, Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari (Twitter/ @GovBorno)

Imam Bukhari ya kai ziyara jihar ta Borno ne, bisa goron gayyata da Dr. Dikwa, shugaban Gidauniyar Al- Ansar Foundation da ke gina jami’a mai zaman kanta ta farko a jihar Borno ya aika masa.

Daya daga cikin limaman Masallacin Makka Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari, ya kai wa gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ziyara.

Yayin ganawarsu da Gwamna Zulum, Imam Bukhari ya ce ya yi farin ciki matuka da yadda jihar Borno take tarbar baki da kuma dadadden tarihin da take da shi na karantar da ilimin Al Qur’ani.

A cewar Bukhari, wanda shi ne shugaban tsangayar koyar da harshen Larabci ga baki a Jami’ar Ummul Qura a Makka, jihar Borno ta yi fice a duniya wajen samar da makaranta Al Qur’ani.

“Farfesa Bukhari ya nuna sha’awar yin mu’amulla da kai, saboda ya kwashe wasu shekaru yana bibiyar ayyukanka da irin ci gaban da aka samu karkashin mulkinka.” Dr. Mohammed Kyari Dikwa, wanda ya zama tafinta ga Imam Bukhari ya ce, yayin da yake fassara kalaman Bukhari da harshen Ingilishi.

Gwamna Zulum (sanye da bakar alkyabba) da tawagar Imam Bukhari (Twitter/ @GovBorno)
Gwamna Zulum (sanye da bakar alkyabba) da tawagar Imam Bukhari (Twitter/ @GovBorno)

Imam Bukhari ya kai ziyara jihar ta Borno ne, bisa goron gayyata da Dr. Dikwa, shugaban Gidauniyar Al- Ansar Foundation da ke gina jami’a mai zaman kanta ta farko a jihar Borno ya aika masa.

Karin bayani akan: Islama, Al Qur’ani, Musulmin, Maiduguri, Imam Bukhari, jihar Borno, Saudiyya, Nigeria, da Najeriya.

A nasa jawabin, Gwamna Zullum ya ce, jihar Borno na da dadaddiyar dangantaka da gwamnati da kuma al’umar kasar Saudiyya, yana mai nuna farin cikinsa da wannan ziyarar da suka kai masa.

“Zuwan daya daga cikin Limaman Masallaci mai tsarki Maiduguri, babban abin farin ciki ne ga daukacin al’umar Musulmin wannan jiha.” In ji Zullum

Zulum ya kuma nemi hadin kai wajen yaki da tsauraran akidu don a maido da zaman lafiya jihar ta Borno da kuma taimakon kasar ta Saudiyya wajen koyar da harshen Larabci da ilimin addinin Islama.

Gwamnan ya kara da cewa, asalin al’umar Kanuri daga kasashen Larabawa suke kafin su yi kaura zuwa yankin jihar ta Borno.

.

XS
SM
MD
LG