Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kunar Bakin Waje a Pakistan


Rahotann dake zuwa daka Pakisan sunce an samu fashewar Bom a wani filin wasa.

Jami’ai a kasar Pakistan sun bada rahoton cewa akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu, wasu bakwai kuma suka jikkata a dalilin harin kunar bakin waken da wani ya yiwa kansa a filin wasannin Tamaular dake Arewa maso yammacin Pakistan.

Anji babban jami’in ‘yan sanda Faisal Mukhtar na fadin cewa ga dukkan alamu an shirya kai harin bom din ne kan cibiyar gungun ‘yan gudun hijira dake kula da yankin Khyber a lokacin da al’ummar yankin ke bada sunayensu domin yin rajista.

Babu wanda yace shike da alhakin kai harin.
XS
SM
MD
LG