Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta Ce Sama da Mutane 100 Sun Mutu A Wata Ambaliyar Ruwa A Nijeriya


Ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya.
Ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya.

Hukumomi a Nijeriya sun ce ambaliyar ta kashe a kalla mutane 102

Hukumomi a Nijeriya sun ce ambaliyar ta kashe a kalla mutane 102 a sashen kudu maso yammacin kasar cikin satin da ya gabata.

Kungiyar Agaji ta Red Cross a Nijeriya t ace dururuwan mutane sun rasa gidajensu bayan da ambaliyar ruwa daga wata madatsar ruwa ta lalata gidaje a birnin Badun, mai tazarar kilomita 150 daga birnin Lagos da ke gaban teku. Ambaliyar ta kuma rusa gadoji uku a yankin.

Hukumomi sun ce rashin tsarin gine-ginen gidaje da kuma karanci ko kuma toshewar kwatamai kan kara hadarin ambaliyar ruwa a irin wadannan wuraren a Nijeriya.

A halin yanzu Nijeriya na dab da yin adabo da damana, wanda kan fara daga watan Mayu zuwa Satumba. Da ma hukumomi sun yi gargadi kan yiwuwar saman ruwan sama sosai a wannan shekarar.

Mummunar ambaliya a wannan kasar ta raba wajen mutane 500,000 da gidajensu a bara.

XS
SM
MD
LG