Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Da Suka Mutu A Harin Bam Na Abuja Ya Karu Zuwa 23


Na’ibar sakatare janar ta MDD, Asha-Rose Migiro, ta ziyarci wasu daga cikin wadanda suka ji raunin a yau lahadi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin bam da aka kai kan ofishinta dake Abuja, babban birnin Nijeriya, ya karu zuwa 23.

Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin bam da aka kai kan ofishinta dake Abuja, babban birnin Nijeriya, ya karu zuwa 23.

Wani kakakin MDD a Najeriya, Martin Dawes, ya fada yau lahadi cewa wasu mutanen su 81 sun ji rauni a wannan harin. Na’ibar sakatare janar ta MDD, Asha-Rose Migiro, ta ziyarci wasu daga cikin wadanda suka ji raunin a yau lahadi a yayin da jami’an MDD da na Najeriya suke ci gaba da bincikensu.

Babban jami’in tsaro na MDD, Greg Starr, yana cikin wadanda suka shiga cikin gudanar da binciken.

Shaidu sun ce wani dan harin kunar bakin wake ya banke wasu kofofi biyu ya shiga cikin harabar ginin majalisar dake Abuja a ranar jumma’a.

Wani mutumin da ya ce wai shi kakaki ne na kungiyar Boko Haram, ya kira VOA yana fadin cewa sune suka kai harin bam din. Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya lashi takobin murkushe ayyukan ta’addanci a kasarsa, yayin da babban sakataren MDD, Ban Ki-moon yace ba za a taba amincewa da irin wannan aiki na ta’addanci ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG