Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Agaji Ta Red Cross Ta Soma Kwashe Mutane daga Aleppo Kasar Syria


Irin mutanen da aka ceto daga Alleppo
Irin mutanen da aka ceto daga Alleppo

Kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross, da wasu kungiyoyi da suke ayyukan jinkai sun ce kimanin farar hula dubu biyu ne aka kwashe daga birnin Aleppo jiya Alhamis, cikinsu har da wadanda suka ji rauni.

Anga jerin-gwanon motocin jigilar majinyata, da wasu manyan safa safa masu launin kore suna barin birnin da yaki ya daidaita, wanda ya kasance cibiyar tarihin musulunci da da al'adun larabawa, kamin yakin basasar da kasar ta shiga ya daidaita birnin.

Motocin sun bi ta yankin da ke hanun gwamnati kamin daga bisani suka shiga wani yankin dake hanun 'yan tawaye a lardin.

Wasu daga cikin fararen hulan sun godewa Allah da ya tserar da su duk da cewa sun bar gawarwakin 'yan uwa da aminai karkashin baraguzan gine-ginen makarantu da gidaje, da kuma wuraren kasuwanci.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG