Accessibility links

Kungiyar Agajin Kiwon Lafiya Ta Fara Duba Lafiyar Yaran Da Gubar Dalma Ta Shafa


Yaran da suka sha ko suka shaki gubar dalma su na jiran ganin likita a Gusau, hedkwatar Jihar Zamfara ranar 9 Yuni 2010

Kungiyar agajin kiwon lafiya ta Doctors Without Borders tace ta fara duba lafiyar daruruwan yara a jihar Zamfara dake Najeriya, wadanda suke fama da cutar gubar dalma da suka kamu dashi a lokutan da sukayi wasa da kasa.

WASHINGTON, D.C - Wakiliyar Muryar Amurka a can Abuja, Heather Murdock ta bada labarin cewa har yanzu dai ana kokarin share wannan guba, amma kungiyar ta Doctors tace lokaci na kurewa saboda damuna na zuwa.

Kafin a fara yi wa yaran da gubar ta shafa magani, dole sai an tsaftace kasar da suke takawa da wasa, idan ko ba haka ba, zasu sake kamuwa da cutar.

Yanzu dai an share shekaru 3 bayan barkewar cutar gubar dalma mafi muni a duniya, ya faru a can arewa maso yammacin Najeriya, kuma yanzu ana cigaba da tsaftace kauyukan da ake tunanin sunfi fuskantar hadari, ta yin amfani da wani fasali mai suna “remediation”.

Wannan fasali dai ya kumshi cire gurbatacciyar kasa, da sauya ta da kasa mai kyau. Amma ruwan sama na cigaba da zuba a wannan waje, kuma shugaban kungiyar Doctors without Borders a Najeriya Simon Tyler yace idan ruwan sama ya cigaba da zuba, to watakila dole ne a dakatar da aikin tsaftace kasar, saboda wahalar aiki da kasa da tabo.

Daruruwan yara ne a wannan yanki suka mutu bayan kamuwa da cutar gubar dalma, sannan wasu da yawa kuma sun samu nakasa na tsawon rayuwarsu.
XS
SM
MD
LG