Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al-Qaida Reshen Afirka Tana Shirin Kai Hari Kasar Ghana?


Shugaban kasar Ghana John Mahama yayi kira ga al'umar kasar cewa kada su tada hankalinsu dangane da rahotanni cewa 'yan ta'adda na kungiyar al-Qaida reshen Afirka tana auna wani sabon hari kan kasar da kuma Togo.

Wannan ya biyo bayan hare haren ta'addanci da aka kai a baya bayan nan kan wasu O'tel a Mali da kuma Burkina Faso. Wadannan hare haren dai wata kungiya mai alaka-da al-Qaida ta dauki alhakin kai su.
A rahoto da Francisca Kakra Forson, ta aiko daga Accra, an sami wadannan bayanan ne daga wasu kasidu na bayanan sirri da aka kwarmato.
A cikin jawabin da yayi ga al'umar kasar ta radiyo jiya Alhamis shugaba Mahama yayi kokarin kwantarwa al'umar kasar hankali.
Ghana ta sanya kasar cikin shirin ko ta kwana cikin watan Maris,bayan da kungiyar al-Qaida arewacin Afirka ta kai hari wani wuri mai farin jini ga 'yan yawon bude ido a Abidjan suka kashe mutane 19.
Kasidun sirrin da aka fallasa, sun ce bayanai da suka samu daga Ivory Coast,ciki harda amsa laifin da mutumin da ya kasance wanda ya jagoranci shirya kai harin, sun nuna cewa maharan sun shiga Ivory Coast ne da wata kirar Jeep, wacce aka yiwa rijista a Nijar. Kasidun suka ce maharan sun boye makamansu ne cikin spare tayar motar.

XS
SM
MD
LG