Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Shabab Da Daukan Yara Aikin Soji - MDD


Yaro ne ke kan gaban wasu sojojin al-Shabab

Wani babban jamiin asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, yace ba za a rasa yara da yawan su yakai 5,000 ba a Somalia wadanda suke cikin sojojin al-Shabab.

Sai dai har yanzu 'yan kungiyar na cigaba da kamfen dinta na daukan yara matasa aikin soja.

A cikin wata hira da yayi da sashen Somaliyanci na wannan gidan Radio, Susannah Price wadda itacekakakin hukumar ta UNICEF tace ci gaba da daukar matasa da kananan yara aikin soja babban abin damuwa ne, domin tana jin adadin sai kara hauhawa yake yi.

Price tace gaskiya wannan abu, abin damuwa ne, domin akwai akalla yara kanana da yawan su yakai dubu 5 a matsayin sojojin wannan kungiyar, kuma dabarar data ke anfani dashi shine na jan hankalin yaran tare da lallashin su, wani lokaci ma har sukan basu abinci da kudi.

Yaran da suka fi zamewa cikin wannan hadarin sau tari yaran dake zaune ne a sannanin ‘yan gudun hijira.Inji Price.

Tace a wani lokaci can baya an kiyasta cewa yawan su yana tsakanin dubu 2 zuwa 3 ne, wani lokaci ma zaka taras yaran, har akwai ‘yan shekaru 9 a cikin su.

XS
SM
MD
LG