Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Al Shabab Ta Kashe Mayakanta


Mayakan Al Shabab

Mayakan Al Shabab a Somalia, sun ce sun kashe wasu mambobinsu biyu, wadanda suka shiga kungiyar daga Kenya, saboda kin bin umurni da kuma sabawa koyarwar addinin Islama.

An dai kashe mambobin biyu ne da suka fito daga Kenya da wani dan Somalia a lokaci guda a yankin Tsakiyar Juba a jiya Juma’a, kamar yadda Sashen Somaliya na Muryar Amurka ya ruwaito.

A can yankin Bay kuma, an kashe wasu mutane hudu a jiya Juma’a, wadanda aka zarga da yiwa gwamnatin Somaliya da Kenya da Amurka ayyukan leken asiri

Daya daga cikin mutanen an zarge shi ne da ba da bayanan da suka kai ga kashe shugaban kungiyar ta Al Shabab Ahmed Abdi Godane ta hanyar yin amfani da jirgi mara matuki a shekarar 2014, mutumin da har ila yau akewa lakabi da Abu Zubayr.

XS
SM
MD
LG