Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al-Shabab Ta Kashe Mutane 15 a Somaliya


 Kwamandan sojojin Somaliya a yankin Baidoa, Abdukadir Ali Dini.
Kwamandan sojojin Somaliya a yankin Baidoa, Abdukadir Ali Dini.

A cigaba da barna da kungiyar Al-Shabab ke yi a Somaliya da kewaye, wannan mugunyar kungiyar ta sake kashe mutane a kalla 15 kuma da alamar adadin mace-macen zai iya karuwa.

Wasu fashe-fashe biyu da su ka auku a garin Baidoa na kasar Somaliya, sun hallaka mutane akalla 15 tare kuma da raunata wasu fiye da 30.

Ministan yada labaran jahar Kudu maso Yamma, Ugas Hassan Abdi, ya ce, "Wasu 'yan kunar bakin wake, saye da jigidar bama-bamai ne su ka kai harin." Ya ce har yanzu jami'ai na tantance adadin wadanda su ka mutu.

Kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Kaida, wadda yankin Baidoa ya kasance karkashinta tsakanin 2009 da 2012 kafin sojojin gwamnatin Somaliya, tare da goyon bayan sojojin Habasha, su ka fatattake ta, ta dauki alhakin kai wannan harin.

Wani wanda ya sha da kyar, ya gaya ma Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, wani dan kunar bakin wake ya jefa gurneti kan wani wurin cin abinci mai cike da jama'a, ya kashe mutane a kalla 5 tare kuma da raunata wasu da dama.

'Yan mintoci bayan harin na farko, sai wani dan kunar bakin waken kuma ya sheko da mota, ya yi karo da otal din Bilan da ke kusa da wurin, ya kashe mutane akalla 7.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG