Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai hari kan wani coci a Nijeriya


Motar da aka kai hari ciki kenan ke cin wuta

Wata kungiyar Islama da ake kira Boko Haram ta dauki alhakin kai harin kunar bakin

Wata kungiyar Islama da ake kira Boko Haram ta dauki alhakin kai harin kunar bakin waken da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 15 a arewacin Nijeriya.

A wani sakon da ya tura wa ‘yan jarida ta kafar ‘email’ kakakin kungiyar mai suna Abul Qaqa ya ce kungiyar ta yi nasarar kai hari a wani coci a birnin Bauchi.

Wani dan kunar bakin wake ne ya tuka wata mota shake da bama-bamai zuwa wata majami’a ranar Lahadi, ya ruguza sashen ginin ya fada kan masu ibada. Sama da mutane 40 sun ji raunuka baya ga wadanda su ka halaka.

A baya ma kungiyar ta Boko Haram ta kai harin bam kan coci-coci, ciki har da wani a kusa da Abuja babban birnin kasar a ranar Kirsimetin da ta gabata. Wancan harin ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 30.

Sakon da ya fito daga Qaqa na zargin jami’an tsaron Nijeriya da boye irin asarar da su ka yi a fafatawarsu da kungiyar. Ya kuma yi gargadin cewa kungiyar za ta kai hari kan ‘yan jaridar da, a ganin kungiyar ta Boko Haram, boyon bayan jami’an tsaro su ke yi a salon rahotanninsu.

Ba a iya tabbatar da sahihancin sakon ba.

XS
SM
MD
LG