Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram Ta Lalata Rabin Asibitocin Jihar Borno


Abubakar Shekau shugaban kungiyar ta'adanci ta Boko Haram

Kimanin rabi cikin asibitocin jihar Bornon Najeriya da ta’addancin Boko Haram ya daidaita sun lalace ko kuma sun daina aiki a cewar wani sabon rahoto.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ko WHO ta fada jiya Laraba a cikin rahotonta tana cewa akalla kashi 35 cikin dari na asibitoci 743 a jihar sun lalace kwatakwata.

Jami’ai suka ce wannan adadi ya bayyana ne a rahoton farko bayan da hukumar kiwon lafiya ta duniya da hukumar kiwon lafiya ta jihar Borno suka yi wani tsarin tattara labarai a kan matsayin aikin kiwon lafiya a jihar.

Wakilin huklumar kiwon lafiya ta duniya a Najeriya Wondi Alemu yace babban aiki da hukumar ta sa a gaba shine ceto rayuka da kare yaduwar cuta tsakanin mutane miliyon shida dake da bukatar jinya cikin gaggawa.

Rahoton yace an kafa kimanin asibitoci na wucin gadi guda dari a jihar Borno don amsa bukatun jama’a na kiwon lafiya ciki har da kananan asibitoci 49 masu kulawan gaggawa a sansanonin ‘yan gudun hijira.

XS
SM
MD
LG