Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram ta tilastawa maza da mata zama sojojin haya - MDD


Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram

Kungiyar Boko Haram ta sace ta kuma maida dubban matasa maza da mata sojojin haya karfi da yaji tun daga shekara ta dubu biyu da goma sha uku. Dakarun Najeriya da na kasar Kamaru suna ci gaba da ceto mutanen da kungiyar take garkuwa da su, sai dai mutanen da ake cetowa sunce tsugune bata kare masu ba.

Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya ko MDD da sojojin kasar Kamaru suna yiwa ‘yan gudun hijiran da suke isa sansanin Minawao tambayoyi.

Hamidou Mahamat yace kungiyar ta sato su ne daga kauyen Kumshe shekaru uku da suka shige.

Yace Kungiyar Boko Haram ta tilasta mashi da ‘yan’uwanshi maza uku su shiga kungiyar. Yace an kashe wadanda suka yi kokarin gudu. Yace mayakan suna kai hare hare a makarantu da kasuwanni suna kuma umartarsu su yi safarar abincin da suka sato da wadansu kayayyaki zuwa sansannansu dake cikin jeji.

Mohammed ya isa sansanin dauke da makami kuma yana ba sojoji hadin kai.

Rundunar sojojin tace ana kama duk wanda aka samu da makami a gurfanar da shi gaban kotun soji ta musamman. Amma ana tsare wadanda suka kai kansu kamar Mohammed wani sansani na musaman inda ake yi masu tambayoyi.

Wata ‘yar shekaru goma sha takwas da ta isa sansanin Minawao bayanda dakarun hadin guiwa suka kai sumame a sansanin Boko Haram tace ta shafe shekaru biyu a hannun kungiyar.

Tace mayakan kungiyar Boko Haram sun tasa keyarsu da ‘ya’yansu zuwa sansanoni. Tace ana sa ‘ya’yansu maza aiki ana kuma koyawa masu amfani da bindiga da nakiyoyi. Tace ana yiwa mata da kananan ‘yammata fyade ana kuma bautar dasu a tilasa masu yiwa mayakan abinci.

Ta rika Magana tana kuka tana rike da danta dan watanni goma sha shida a hannu da tace bata san ko wanene ubansa ba.

Alain Mvago wani babban jami’in soja a yankin yace ‘yan gudun hijiran da suka tagayyara suna samun shawarwari da kuma kula ta musamman.

XS
SM
MD
LG