Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Sauka Daga Mulki


Kungiyar Dattawan Arewa

Duk da gangarar karewar wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta ce wajibi ne shugaban kasa ya ajiye mukamin shi saboda gazawar da ya yi na kare rayukan mutane da dukiyoyi.

KADUNA, NIGERIA - Dama dai a can baya kungiyar Dattawan Arewacin Najeriyan ta taba kira akan shugaban kasa ya sauka daga mukamin shi, sai dai wannan karon ta ce ba shawara ta ke bayarwa ba, dole ne shugaba Muhammadu Buhari ya sauka tun da ya gaza.

Mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewacin Najeriyan Dr. Hakeem Baba Ahmed ya ce kasar ce ke cikin halin tsamin tsaro.

Sai dai tsohon Dan-majalissar Dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani na Jam'iyyar PDP ya ce duk da baya goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari amma bai kamata a ce ya sauka ba.

Maganar matsalar tsaro da matsin rayuwa dai na cikin manyan dalilan da masu sukar gwamnatin shugaba Buhari ke yawan bayarwa, sai dai kuma gwamnatin ta ce tana matukar kokarin kawo karshen matsalolin da ke damun wannan kasa.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti:

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya Ta Bukaci Shugaba Buhari Da Ya Sauka Daga Mulki
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG