Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Yi Shelar Tsayawarsa Takarar Shugaban Kasa


A ranar Litinin ne Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa, lokacin da Shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, zai sauka daga mulki.

An fara da zaben shi ne a matsayin mataimakin Buhari a shekarar 2015. Osinbajo ya bayyana hakan ne bayan an shafe watanni ana cece-kuce kan ko zai gaji ubangidansa ko a'a.

A wata sanarwa da babban Lauyan mai shekaru 65 kuma tsohon malamin jami’ar ya fitar, ya ce shekarun da ya yi a karkashin Buhari ya sa ya zama mutumin da ya fi dacewa da wannan aiki.

“Don haka ne a yau, cikin tawali’u, na bayyana aniyata ta tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin laimar babbar jam’iyyarmu ta All Progressives Congress,” inji Osinbajo.

Ya yi alkawarin ci gaba da manufofin Buhari da shirye-shiryensa da suka hada da manya-manyan ayyuka na sabbin hanyoyi da jiragen kasa.

Wani muhimmin batu da ke gaban zaben watan Fabrairun 2023 shi ne batun tsaro, inda sojojin Najeriya ke fafatawa da masu tayar da kayar baya a yankin arewa maso gabas, da kungiyoyin masu aikata laifuka a yankin arewa maso yamma da kuma rikicin 'yan aware a yankin kudu maso gabas.

Osinbajo ya bi sahun ‘yan takarar jam’iyyar APC mai mulki domin neman tikitin jam’iyyar.

Tuni dai jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu shi ma ya bayyana cewa zai tsaya takarar. Osinbajo ya yi aiki a karkashin Tinubu a matsayin kwamishinan shari’a a Legas na tsawon shekaru takwas.

Sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC sun hada da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi.

Ana sa ran jam’iyya mai mulki za ta zabi wanda zai rike mata tuta a watan Yuni kuma dan takarar zai fuskanci duk wanda ya fito daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, mai shekaru 75, wanda ya taba tsayawa takarar shugaban kasa sau biyar, a watan jiya ya bayyana cewa zai sake tsayawa takara a jam’iyyar PDP.

Bisa ga ka’idar siyasar Najeriya da ba a rubuce ta ke ba ita ce, ana ganin fadar shugaban kasa za ta tabbatar da karba-karba tsakanin ‘yan arewacin kasar da galibinsu Musulmi ne da kuma Kudancin kasar da Kirista ke da rinjaye, a kokarin raba madafun iko daidai-wa-daida.

Bayan Buhari, wanda Musulmin Arewa ne, ya kammala wa’adinsa biyu a shekara mai zuwa, ‘yan Kudu da dama sun ce ya kamata Shugabancin ya koma yankinsu.

XS
SM
MD
LG