Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar El-Zakzaky Ce Gwamnatin Kaduna Ta Haramta - El-Rufai


Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky

Cikin firar da yayi da Muryar Amurka gwamnan Kaduna ya bayyana cewa gwamnatinsa bata hana addinin Shi'a ba saboda gwamnati bata da ikon hana wani addini amma kungiyar El-Zakzaki ce ta haramta

Duk wanda ya fito yace shi dan kungiyar El-Zakzaki ne to yayi laifi saboda gwamnati bata amince da kungiyar ba.

Dokar da jihar tayi anfani da ita ta samo asali ne tun 1963 lokacin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto kuma firimiyan lardin arewacin Najeriya wanda shi ma yayi anfani da ita a duk lokacin da ake son tada zaune tsaye.

Jihar tayi dokar ne ba domin Shi'a ba saboda akwai wasu kungiyoyin Shi'a guda biyu kuma ba'a hanasu yin addininsu ba ama ba sa tare da El-Zakzaki. Gwamnatin Kaduna bata da wata matsala da wadannan kungiyoyin biyu. Gwamnati bata hanasu yin addininsu ba domin babu wata gwamnati da zata hana wani yin addininshi bisa ga dokar Najeriya.

Gwamnatin Kaduna ta hana kungiyar da ta fito karar tace bata yadda da mulkin Najeriya ba. Bata yadda da shugabancin Buhari ba kuma bata yadda da shugabancin gwamnan jihar ba.

Kungiyar El-Zakzaki tana da gwamnanta. Kungiyar tace babu ruwanta da dokokin Najeriya. Duk dokar da aka yi a kasar zasu karya suyi abun da suka ga daman yi. Gwamnan yace duk wani mai shakkan abun da ya fada ya je Gellesu ya tambayi mutanen wurin. Kungiyar ta kutunka ma jama'a a wurin.

Kungiyar El-Zakzaki nada sojojinta masu sanya kayan sojoji tare da dimbin makamai kuma suna horas dasu. Kungiyar na rufe hanya tare da shiga makarantu su kwana cikinsu dole. Babu ruwansu da dokokin kasa.

Duk kungiyoyin addinai sun yi rajista walau na musulunci ko na kiristanci amma kungiyar El-Zakzaki bata taba rajista ba da gwamnati kuma ta ki tayi. 'Yan kungiyar basu amince da gwamnatin Najeriya ba bare suyi rajista.

Gwamnati ba zata yadda da wata kungiyar da tace ita ce gwamnatin kanta, irin wannan halin ne ya jawo tashin hankali da sojoji. Gwamnan ya ce idan basu dauki matakan da suka dauka ba za'a cigaba da samun tashin hankali.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:30 0:00

XS
SM
MD
LG