Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar EU Ta Bukaci Trump Ya Canza Ra’ayi Kan Hukumar WHO


Trump-Breathing Machines
Trump-Breathing Machines

Kungiyar Tarayyar Turai na kira ga Shugaban Amurka Donald Trump da ya canza shawarar da ya yanke ta daina daukar nauyin Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) a daidai lokacin da ake fama da annobar coronavirus wanda ke neman yin tsanani a Indiya da wasu wurare.

Trump ya bayyana shawarar da ya yanke ranar Jumma’a, yana mai zargin WHO da rashin daukar matakan da su ka dace kan wannan annobar da ta addabi duniya, da kuma zama ‘yar koren China.

European Commission President Ursula von der Leyen speaks during a joint press conference after a G7 Leaders' videoconference on COVID-19 at the EU headquarters in Brussels on March 16, 2020. - Ursula von der Leyen on March 16 proposed that the EU…
European Commission President Ursula von der Leyen speaks during a joint press conference after a G7 Leaders' videoconference on COVID-19 at the EU headquarters in Brussels on March 16, 2020. - Ursula von der Leyen on March 16 proposed that the EU…

(Shugabar EU Ursula von der Leyen)

Shugabar EU Ursula von der Leyen da kuma Ministan Harkokin Wajen EU Josep Borrell sun fadi a wata rubutacciyar takarda ta hadinn gwiwa a jiya Asabar cewa, “Ya kamata WHO ta cigaba da zama wace za ta iya jagorantar duniya wajen daukar mataki kan wannan annobar da ma duk wadda ka faru nan gaba.”

“Ya kamata a kauce ma duk wani matakin da ka iya yin nakasu ma hadin kan duniya don a samu sakamakon bai daya ,” a cewar jami’an na EU. Su ka kara da cewa, “Mu na kira ga Amurka da ta canza shawarar nan da ta yi shelar daukarta.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG