Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar EU Ta Ce Rasha, China, Amurka Su Na Mata Barazana


 Donald Tusk
Donald Tusk

Wadannan kalamai na sa sun fito ne a wata wasika da ya aikewa shugabannin kungiyar 27, gabanin taron kolin kungiyar ta EU da za a yi ranar Juma'a a Malta.

Tusk ya ce “Sauyin da aka samu a Washington ya saka kungiyar tarayyar turan a cikin wani mawuyacin hali, saboda samun sabuwar gwamnatin na saka alamar tambaya a harkokin wajen Amurka da ta dade ta na yi har na tsawon shekaru 70.”.

Trump dai ya dage akan cewa Amurka ce farko a duk wani abu da za a yi, sannan ya na kalubalantar ko mambobin kungiyar tsaro ta NATO su na ba da gudunmuwarsu kamar yadda dangantakar ta bukata."

Tusk ya kuma kare Tarayyar Turai ya na mai cewa ba ta taba fuskantar hadari da kalubale ba, kuma yankin na bukatar ya nuna jajircewa da himma da kuma nuna goyon bayan juna a siyasance.

Ya ce dole ne kungiyar tarayyar turai ta tsaya tsayin daka da martabarta wajen ganawa da Amurka da Rasha da China da kuma Turkiya , kuma kada su ba da kai buri ya hau kan batutuwan da suka shafi nuna kyama da son rai, domin hakan ya sabawa al'adar dunkulewar nahiyar ta Turai.

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG