Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar EU Ta Tallafa Wa Wasu Kungiyoyin Nijar Da Miliyoyin CFA


Bukin Tallafa wa Kungiyoyi a Nijar
Bukin Tallafa wa Kungiyoyi a Nijar

A safiyar ranar Litinin 12 ga watan Oktoba ne aka yi bukin bayar da tallafin kudaden kungiyar Tarayyar Turai ga wasu kungiyoyin cikin gida a Nijar masu ayyukan kyautata rayuwar al’uma. 

Kimanin kungiyoyin cikin gida 10 ne aka rarrabawa wadannan kudaden tallafin da yawansu ya haura miliyan 2,000 na CFA bayan aikin tantance wadanda suka cancanci samun wannan tallafi daga kungiyar Tarayyar Turai da ake kira EU a takaice.

Jakadiyar EU a Nijar, Dr. Denisa Helena Ionette, ta ce makasudin wannan shiri shine bai wa kungiyoyin farar hula damar gudanar da aiki kamar yadda ya dace.

Kungiyar kare hakkin ‘yan cirani ta ONG JIMED na daga cikin wadanda suka samu wannan tallafin. Shugaban kungiyar Manou Nabara, ya ce za su yi aiki da kungiyoyin al’uma da ke Agadaz, da Tahoua, da sauransu saboda su ma su samu damar gudanar da ayyukansu don a sami jituwa tsakanin ‘yan cirani da mutanen garin da suke tararwa.

Ministan Ayyukan ci gaban karkara na Nijar, Abdou Amani, ya gargadi shugabanin wadannan kungiyoyi akan maganar kashe kudaden da suka karba ta hanyar da ta dace.

Amani ya kara da cewa wannan kudade na al’uma ne ba wai an basu ba ne domin su je su yi sha’anin gaban su, dan haka gwamnati za ta bi diddigi ta ga yadda suka kashe kudaden.

Wannan shine zagaye na 3 da kungiyar EU ke bai wa kungiyoyi masu zaman kansu irin wannan tallafi na daukar dawainiyar kudaden ayyukan da suka tsara yi wa jama’a a karkasahin shirin PASOC.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG