Accessibility links

Kungiyar Filani Makiyaya ta Koka da Kisan Gillar 'Ya'yanta a Benue


Gwamnan Benue Gabriel Suswan

Rigingimu da Filani a sassan Najeriya sai karuwa ya keyi inda suke kashe mutane su kuma a kashesu lamarin da ya sa suka koka kan abun da a keyi masu a Benue.

Kungiyar Filani Makiyaya ta Miyetti Allah ta koka game da kisan gillar da tace ana yiwa Filani a jihohin Benue da Taraba da Nasarawa.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar wadda mataimakin kungiyar a Najeriya Alhaji Useini Boso ya sanyawa hannu yace a yanzu haka an kori ilahirin Filani daga jihar ta Benue kana ana binsu ana yi masu kisan gilla a jihohin Taraba da Nasarawa.

Sanarwar ta zargi gwamnatin jihar Benue da bada izinin korar ilahirin duk Filani daga jihar. Mataimakin shugaban kungiyar Alhaji Boso ya kara haske kan maganar. Yace suna mamaki yadda gwamnan Benue da sauran manyan jihar 'yan siyasa suka yadda a kori Filani daga jihar. Yace lamarin ba maganar makiyaya da manoma ba ne. Duk al'ummomin jihar da matasa da manoma da 'yan kasuwa suka tashi suka kori Filani. Yace su 'yan Najeriya ne kuma Benue tana cikin Najeriya domin haka ina ake son su je?

Alhaji Boso yace bayan an koresu shanun da suka salwanta sun kai dubu goma a cikin wannan shekarar kawai. Suna bin Filani zuwa cikin jihohin Nasarawa da Taraba suna kashesu suna kuma sace masu shanu.

Kungiyar ta yi kira da a kawo karshen kisan gillar da ake yiwa Filani. Sun bukaci gwamnatin tarayya ta bincika ta yi hukuncin da ya kamata bisa gaskiya.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

XS
SM
MD
LG