Accessibility links

Kungiyar Fulani ta Kiristoci a Najeriya ko FULCAN ta Kuduri Aniyar Sasanta Al'ummomi


Fulani makiyaya

Kungiyar Fulani ta Kiristoci a Nageriya ko FULCAN a takaice, ta kuduri anniyar sasanta al'ummomi a Najeriya domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Ganin yadda tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma ke jawo rashin fahimta da fadace fadace tare da hallaka rayuka da dukiyoyi tsakanin al'ummomi yasa kungiyar ta FULCAN tace yanzu fa lokaci yayi da zata tashi haikan wajen wayar da kawunan mutane akan alfanun dake tafe da zaman lafiya.

Shugaban FULCAN Rabaran Buba Aliyu ya bayyana wasu cikin ayyukan da kungiyar keyi domin sasanta al'umma. Yace suna taimakon mutane a sashen asibiti. Suna taimakon mutane akan rigingimun dake tashi tsakanin Fulani da wasu kabilu wajen sasantawa. Suna kuma duba yadda gwamnati zata san da Fulani. Kabilu da dama idan suna magana suna cewa bafullatani baya yafewa. Alhali kuwa idan an karanta littafi mai tsarki Yesu Almasihu shi ne shugaban sulhu. Aikinsu ne su kawo sulhu tsakanin wadanda suke gaba da juna.

Ta dalilin kungiyar suna son su yi maganin tashin hankali domin a daina cewa Fulani su ne 'yan ta'ada. Ana cewa Fulani su ne suke kashe kashe. Su ne suke kai hariakan mutane. Cigaba da gaba ba hanyar Almasihu ba ce. Almasihu yace ramako na Allah ne. Wato, ma'ana, a yafe ma juna. Sabili da haka su da suka yi karatu zasu wayar da kawunan kowa cewa bafullace ba dan ta'ada ba ne.

Shugaban ya kuma shawarci al'ummarsa cikin harshen fulatanci.

Ga rahoton Zainab Babaji.

XS
SM
MD
LG