Accessibility links

Kungiyar Hadin Kan Kirista Ta Soki Matakan Shugaba Jonathan Dangane Da Ahuwa


WASHINGTON, D.C - Sakataren kungiyar Rev. Dr. Musa Asake ya nanata goyon bayan yi wa kungiyar ‘yan bindiga da ake kira Boko Haram afuwa , amma kungiyarshi tana gani kamar yafi dacewa gwamnati ta fara tattaunawa da ‘ya’yan kungiyar tukunna, a ji matsalar su, kuma a ji daga wace kasa suke.

Kungiyar ta yi kira da gwamnati da saurari mutanen da tashin hankulan ya shafa, musamman ma wadanda suka yi asarar rayuka da kadarori.


Dr. Asake ya rufe da cewa yana kira da kwamitin da gwamnati ta kafa na yin sulhu da ‘yan bindigan, da yayi aikin da zai kawo karshen tashin hankali, da zaman lafiya mai dorewa a Najeriya.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG