Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar IS tana kira ga magoya bayanta a fadin duniya su kai hare hare a wannan watan azumi.


ISIS
ISIS

Kungiyar IS tana kira ga magoya bayanta a duk fadin duniya su kai hare hare a wannan watan mai tsarki na azumi.

Wani da yake kiran kansa kakakin kungiyar ne ya yi wannan kiran a shafin sandarwar internet na kungiyar ISIS da ake kira Telegram.

Kasashen da suke shirin kaiwa harin sun hada da Amurka, da Rasha da Australia da Iran da Iraq da Syria da Philipins, da kuma kasashen Turai.

Kungiyar IS ta dauki alhakin tagwayen hare haren da aka kai a Tehran da aka hallaka mutane goma sha biyu. Kakakin ya yi kira da a kara kai hare haren bom a Iran, da cewa, yanar gizo tafi kasar karfi.

Kungiyar IS ta saba kira ga magoya bayanta su kai hare hare lokacin azumi, da aka fara ranar ishirin da shida ga watan Mayu, da za a kuma gama ranar ishirin da hudu ga watan Yuni .

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG