"Idan ka dubi abunda ya faru a tashar jirgin sama na Turkiyya, wadannan farmaloli ne da nakiyoyi na kunar bakin wake. Bashi da wani wahalar hadawa," Brennan ya fada lokacin da yake magana da sashen labarai na kamfanin Yahoo.
Zuwa yanzu dai babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin, amma hukumomi a Turkiyya tuni suke zargin gungiyar ta 'yan ta'adda, waato ISIS da kai hare-haren.
Firayim Ministan Turkiyya Binali Yildrim, yace ana ci gaba da bincike, amma shaidar da aka samu tana nuni da cewa wannan aikin ISIS ne. Firayim Ministan yace ta yiwu harin martani kan yunkurin da kasar take yi na inganta dangantaka da kasashen Rasha da Isra'ila.
Mutane 42 ne suka halaka, wasu 239 kuma suka jikkata, lokacinda 'yan kunar bakin waken uku suka bude wuta da manyan bindigogi sannan daga bisani suka tarwatsa kansu