Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin da Aka Kai Tunisia


Masu aikin agaji suna ceton wani da ya jikata sanadiyar harin

Kungiyar ISIS mai tsatsatsauran ra'ayin addini ta dauki alhakin harin da aka kai Tunisia

Kungiyar nan ta masu tsatstsauran ra'ayin addini da ake kira ISIS a takaice jiya Alhamis ta dauki alhakin mummunar harin da aka kai a wani dakin ada kayan tarihi a Tunisia, wanda yayi sanadiyyar kisan mutane 23 galibinsu 'yan yawan bude ido.

A cikin sanarwar da kungiyar ta bayar ta kira harin da cewa "farmaki mai albarka kan wani sansanin kafirai da barna a kasar Musulman Tunisia". An wallafa sakon ne a wani dandalin internet inda kungiyar take bayyana sakoninta, kuma wata kungiyar lura da harkokin tsaro a nan Amurka da ake kira SITE tace da alamun sakon yana da sahihanci.

Tunda farko jiya Alhamis, hukumomin kasar Tunisia suka ce sun kama mutane tara dangane da harin da aka kai wurin adana kayan tarihin. Sai dai basu bada bayanai kan mutanen da aka kaman ba.

Jami'an tsaron kasar sun harbe suka kashe 'yan binidgan biyu a wurin da aka kai harin ranar Laraba, daga bisani suka ce suna neman wasu da sukeda hannu a kitsa makarkashiyar kai harin.

An bayyana sunayen 'yan binidgar, wato Yassine Laabidi da Hatem Kachnaoui.

Cikin wadanda aka kashe a harin akwai 'yan kasashen waje 20 wadan da suka je kasar yawon bude ido, da kuma 'yan kasar Tunisiyan uku, kamar yadda bayanai da jami'an gwamnatin kasar suka bayar suka nuna.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG