Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin da Aka Kaiwa Wasu Mata Biyu a Faransa Jiya


Wurin da aka kai hari inda aka rufe gawarwakin da farin mayafi

Jiya Lahadi a Marseille dake kasar Faransa wani ya hallaka mata biyu da wuka kafin wasu jami'an tsaro su gama dashi

: Kungiyar ISIS ta yi ikirarin kai wani harin ta'addanci, na daba ma wasu mata biyu wuka har lahira, a wata tashar jiragen kasa da ke Marseille (pron: Marsey), a kasar Faransa jiya Lahadi.

Kungiyar mai tsatsauran ra'ayi ta yi ikirarin ne ta kafar labaranta a hukumance.

Wani mutum, wanda ya daga murya ya na cewa, "Allahu Akbar," ne ya daba ma matan biyu wuka, kafin sojojin Faransa su ka bindige shi har lahira.

'Yansanda sun rufe tare da killace tashar sannan nan da nan Ministan Cikin Gida, Gerard Collomb ya ruga zuwa Marseille.

Masu gabatar da kara a madadin gwamnatin Faransa sun fara bincike irin na harin ta'addanci, to amma har yanzu Collomb bai ayyana harin a matsayin na ta'addanci ba a hukumance.

Hoton bidiyon da 'yansanda su ka bayyana ya nuna wanda ake zargin na daba ma mace ta farko wuka, sai ya bace, can sai ya sake bulla ya kai hari kan ta biyun.

haka kuma mutmen ya ruga ya dumfari sojoji sai su ka bude masa wuta su ka kashe shi. Har yanzu ba a bayyana ma jama'a ko waye maharin da kuma wadanda ya kashe din ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG