Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Kai Hare-Haren Paris


'Yan jarida su na daukar hoto a kofar wani gidan cin abinci

Kungiyar ta ce hare-haren da suka kashe mutane akalla 127 a Paris, ramuwar gayya ce ta hare-haren da ake kaiwa daga sama a kan mayakanta a kasashen Iraqi da Syria

Kungiyar ISIS, wadda ake kira Daesh da larabci, ta dauki alhakin munanan hare-haren da aka kai lokaci guda cikin daren Jumma'a a birnin Paris, inda a yanzu aka dauki karin matakan tsaro na hana sake abkuwar hakan.

A yau asabar kungiyar ta ayyana cewa hare-hare guda 6 da aka kaddamar a lokaci guda aka kashe mutane akalla 127 a Paris, martani ne ga hare-haren da ake kaiwa ta sama a kan mayakanta a Iraq da Syria. Sakon yace Faransa da magoya bayanta zasu kasance a saman jerin sunayen da kungiyar ISIS zata rika aunawa don kai musu hare-hare.

Wannan sakon daukar alhakin an rubuta shi da harsunan larabci da kuma faransanci, aka yada ta yanar gizo. Babu wata hanyar tabbatar da sahihancin wannan sakon nan take, sai dai yana dauke da hatimin ISIS, sannan yayi kama da wasu sakonnin kungiyar na baya. Kwararru kan harkar ta'addanxci dai ba su tababar sahihancin wannan sakon.

Sanarwarf ta ISIS, ta ce "Warin matattu ba zai gushe daga hancinsu ba (su shugabannin Faransa) muddin suka ci gaba da kasancewa a kan gaba a rundunar masu yaki da Musulunci, su na zagin annabinmu, suna alfahari cikin kasar Faransa da cewa suna yaki da Musulunci, sannan suna kai hare-hare a kan Musulmi a daular Musulunci da jiragen samansu wadanda ba su da wani amfani a a tituna da rubabbun lunguna na Paris."

Shugaba Francois Hollande ya lashi takobin farauto wadanda suka kai hare-haren, yana mai cewa ba za a yi musu rangwame ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG