Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu makaman da Amurka ke jefawa kurdawa daga sama sun fada hannun mayakan ISIS

‘Yan gwagwarmaya a Syria sunce wasu makamai da alburusai da Amurka ta jefawa mayakan kurdawa ta sama, sun fada hannun mayakan ISIL.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Syria dake Britaniya tace jiya Talata mayakan sa kai suka wawashe makamai da dakarun sojin saman Amurka suka jefa ta jiragen yakin sama a daren Lahadi.

Hotunan bidiyo daga wata kungiya mai goyon bayan ISIL sun nuna wani mayaki wanda ya rufe fuskarshi yana duba makamai, inda ya bayyana farin cikinshi da annashuwa.

XS
SM
MD
LG