Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Islama ta Muslim Brotherhood ta yi ikirarin fara galaba


Zaben Misra

A yayin da ‘yan Misra ke kammala kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa

A yayin da ‘yan Misra ke kammala kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa na tsawon kwanaki biyu mai cike da tarihi, alamun farko na nuna cewa dan takarar kungiyar Islamar nan ta Muslim Brotherhood ne kan gaba cikin ‘yan takara biyar da su ka fi yin fice.

Wani mai magana da yawun dan takarar kungiyar ta Muslim Brotherhood Mohammed Morsi, ya fadi jiya Alhamis cewa dan takarar ya zarce ne a wani kuri’ar jin ra’ayin wadanda su ka yi zaben da jami’an yakin neman zaben kungiyar su ka gudanar. Kowanne daga cikin ‘yan takara 5 da ke kan gaba ya nuna kwarin gwiwar yiwuwar yin nasara kodayake da dama sun yadda cewa Morsi ya fara zarce su.

Ba a iya tantance sahihancin sakamakon kungiyar ta Brotherhood ba. Wasu gidajen talabijin na yankuna ma sun yi amfani da nasu kuri’un jin ra’ayin wadanda su ka yi zaben, wajen ayyana Morsi a matsayin na gaba, su kuma manyan masu kalubalantarsa su Ahmed Shafiq da Hamdeen Sabani ke kokarin zuwa na biyu.

Za a sanar da cikakken sakamakon zagaye na farko na zaben ranar Talata. An tsaida da ranakun 16 zuwa 17 ga watan Yuni, don zaben fidda gwani muddun mutane biyu su ka yi kunne doki. Za a bayar da sanarwar wanda ya ci zaben ran 21 ga watan Yuni.

XS
SM
MD
LG