Accessibility links

Kungiyar Kasashen Afirka Za Ta Bukaci Taimakon Majalisar Dinkin Duniya Game Da Kasar Mali

  • Halima Djimrao-Kane

Taron tattaunawa game da matsalar tsaro a kasar Mali

Kungiyar kasashen Afirka za ta mika bukata ta musamman

Taron kolin shugabannin kasashen Afirka yayi kira ga MDD ta bada cikakken goyon bayan yin amfani da karfin soja wajen maido da zaman lafiya a Arewacin Mali da yanzu ya fada hannun mayakan ‘yan tawaye.

Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afirka, da kungiyar ECOWAS da kuma MDD jiya Alhamis suka cimma daidaituwar umartar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da ta mika bukata ta musamman ga kwamitin sulhu da tsaro na MDD ya bada iznin tsoma hannu a rikicin kasar Mali domin maido da mutumcin kasar tare da sake maida kasar dunkulalliya.

Shugaban kungiyar ECOWAS, Kadre Desire Quedrago, yace lallai kam yankin Arewacin Mali al’amura na kara kazancewa matuka, kuma idan ba an gaggauta daukan wani matakin yin amfani da karfin soja ba, al’amuran tsaron yankin za su lalace baki daya.

XS
SM
MD
LG