Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Ta Goyi Bayan Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa


Hotunan alkaluman tattara bayanai dangane da cin hanci da rashawa da wasu kungiyoyi sittin masu zaman kansu suka kaddamar a Abuja. Kungiyoyin sun hada kansu domin su bada tasu gudunmawar wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

kungiyar kwadagon Najeriya tare da sauran kungiyoyin sa kai sun gudanar da wani gangami a fadin kasar domin nuna goyon bayan yunkurin gwamnatin Najeriya, na yaki da ayyukan rashawa da cin hanci.

An dade dai ana zargin ma’aikata da hannu dumu dumu cikin ayyukan cin hanci da rashawa a Najeriya, mutane da dama na tuhumar ma’aikata da nunawa ‘yan siyasa da sauran jami’ai hanyoyin da zasu bi wajen batar da sawun dukiyar ‘kasa, a yayinda awani lokutan ma ma’aikatan ne a tsakanin su ke tsara dabarun fitar da dukiyar al’umma. Yayin da a hannu guda kuma akan samu wasu ma’aikata da neman na goro kafin ya aiwatar da wani aiki da aka rataya a wuyansa.

Tuni dai masana kan lamuran kungiyoyin kwadago da nagartar aiki suka fara sharhi da tsokaci game da ko gangami ka iya tasiri ko kuma a’a wani masani kan fasahar kwadago da sha’anin ma’aikata Mallam Mansur Datti na kwalejin fasaha ta Kano, yace gangamin da akayi wani yunkuri ne da ma’aikatan Najeriya ke neman wanke kansu daga zarge zarge rashawa a Najeriya. inda yace “gyaran zukata na ma’aikata baki daya, kowa ya dauka cewar amana ce a hannun sa kowa ya dauka kuma lokaci yayi da za’a canza.”

Sai dai acewar kwamarad Alhassan Uba Idris, wani tsohon ‘dan gwagwarmayar kwadago a Kano yace babu shakka yunkurin na da kyau, amma kwalliya ba zata kai ga biyan kudin sabulu ba har sai ita kungiyar kwadagon da shugabannin ta sun fara yaki daga cikin gida.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG