Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Ta Najeriya NLC Ta Yi Alla-Wadai Da Kara Farashin Man Fetur Da Gwamnati Ke Shirin Yi A Shekarar 2022


Shugaba Buhari da Kungiyar Kwadago

Shugaban Kungiyar, Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar wa manema labarai mai taken: Ma’aikatan Najeriya ba za su yi na’am da wannan mataki ba.

Batun hakan ya biyo bayan sanarwa da babban daraktan kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, Mele Gyari ya yi na cewa akwai yiwuwar farashin mai ya tashi zuwa N340 a watan Fabrairun shekarar 2022 sakamokon cire tallafin man fetur

A cewar sa abin dariya ne a ce gwamnati ta yi alkawarin raba wa 'yan Najeriya miliyan 40 kyautar N5000 don rage zafin da Karin farashin zai haifar a garesu

Ayuba Wabba ya bayyana cewa akwai rainin hankali cikin lamarin kuma haka ya saba yarjejeniyarsu da Gwamnati

Ya ce "Yarjejniyar da Gwamnatin Najeriya ta yi da jama'arta, musamman ma'aikata, shi ne an dakatar da maganar tallafin mai har illa ma shaa'aLLahu."

''Sakamakon sabbin maganganun da muke ji tsakanin Gwamnati da kungiyoyin kasashen waje, NLC na sanar da cewa ba zata yarda da cire tallafi ba’’

Shugaban NLC ya ce kokarin da Gwamnatin ke yi a kwatanta farashin mai a Najeriya abu ne da ba zai sabu ba.

A ranar Talatar da ta gabata ne, yayin wani taron kaddamar da rahoton Bankin Duniya, Ministar kasafin kudi da tsare tsare na kasa, Zainab Ahmad Shamsuna ta bayyana cewa Gwamnatin tarayya za ta rika kashe Naira biliyan N200 a wata wajen raba wa talakawan kasar kudi domin rage zafin da cire tallafin mai zai haifar saboda, a cewarta, idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.

Ministar ta ce talakan Najeriya mutum guda milyan 30 zuwa 40 za a rika bai wa wannan kudi wata-wata, amma ta ce sai an cire tallafin za a san adadin 'yan Najeriya da za su samu wannan kudi.

XS
SM
MD
LG