Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Tayi Zanga zanga A Abuja


Ministan Makamashi, Ayyuka da Samar da Gidaje Babatunde Fashola

Kungiyar kwadagon Najeriya reshen Abuja ta fantsama cikin zanga zanga saboda kin biyan ma'aikata hakinsu da kuma zargin nuna wariya da ministan ma'aikata yayi inda suka ce ya biya ma'aikatan da suka fito daga bangarensa ya bar sauran.

Kwamred Nasiru Kabir jami'in kungiyar kwadago ta kasa ya yiwa Muryar Amurka bayani akan makasudin zanga zangar.

Yace rashin adalci da wulakanta bil Adama su ne sanadiyar zanga zangar. A ma'aikatar aiki da wutar lantarki da gidaje dake karkashin Mr. Babatunde Fashola a matsayin minista, ana zargin akwai nuna rashin adalci. Ya hana biyan wasu ma'aikata amma an wayi gari ya biya wasu da suka fito daga bangarensa, wato 'yan kudu maso yammacin Najeriya. Amma kuma ya rabu da sauran mutanen da ba nashi ba.

Dangane da bin hanyar lalama, Kwamred Kabir yace kungiyar kwadago ta zauna ta tattauna , tayi magana dasu babu abun da aka yi sai ma makawa ma'aikatan dokoki iri iri. Yace sun taba rubuta wasika zuwa fadar shugaban kasa akan shi Fashola.

Wasu ma'aikatan da suka shiga zanga zangar su ce tun shekarar 2011 aka yi masu karin mukami amma ahar yau ba'a biyasu ba. Akwai alawus daban daban da ba'a biya ba.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG