Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Za Ta Yi Zanga-zanga Saboda Tsadar Rayuwa


Wat zanga-zangar kungiyoyin kwadago a Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)
Wat zanga-zangar kungiyoyin kwadago a Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)

NLC ta ce za ta shiga yajin aikin a ranakun 27 da 28 na wannan wata na Fabrairu don jan hankalin hukumomi kan yadda ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa.

Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta ayyana shirin gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu saboda tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar.

Shugaban kungiyar Comrade Joe Ajaero ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin ganawa da manema labarai a Abuja, babban birnin kasar.

A cewarsa, kungiyar za ta yi zangar-zangar a ranakun 27 da 28 na wannan wata na Fabrairu don jan hankalin hukumomi kan yadda ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa.

Kungiyar har ila yau ta ce za ta yi gangamin ne saboda tabarbarewar tsaro a sassan kasar.

Wata zanga-zangar da NLC ta yi a baya
Wata zanga-zangar da NLC ta yi a baya

Matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa ta yi kamari a sassan kasar ciki har da birnin Abuja da fadar shugaban kasa ta ke.

Ajaero ya ce zanga-zangar za ta wakana ne mako guda bayan cikar wa’adin makonni biyu da kungiyar ta bai wa hukumomin Najeriya wanda zai kare a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Matsalar hauhawar farashin kayayyaki musamman na kayan masarufi ya jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali yayin da darajar Naira ke ci gaba da faduwa.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu

Hukumomi sun ce suna daukan matakan da suka dace ciki har da fito da abinci daga rumbunan gwamnati don a rabawa jama’a.

A makon da ya gabata, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarni a fitar da tan 102,000 na shinkafa da masara daga rumbun adana abinci na tarayya.

A ranar Alhamis ya gana da gwamnonin jihohin kasar 36 don lalubo hanyoyi da za a magance matsalolin kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG