Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Lauyoyin Nijar Na Bikin Cika Shekaru 30 Da Kafuwa


Taron Kungiyar Lauyoyin Nijar
Taron Kungiyar Lauyoyin Nijar

Kungiyar lauyoyi a jamhuriyar Nijar na bikin cika shekaru 30 da kafuwa, hakan yasa lauyoyin ke amfani da wannan dama domin tantaunawa akan hanyoyin tabbatar da ‘yancin ma’aikatar shari’a a kasar.

Taron bikin dai ya mayar da hankali ne kan wasu muhimman batutuwa uku wadanda suka hada da bude fagen sabuwar shekarar lauyoyi, sai kuma bitar ayyukan da kungiyar ta gudanar a tsaron shekaru 30, da kuma mayar da hankali wajen ganin an kawar da duk wani katsalandan din da fannin shari’a ke fuskanta.

Da yake bayaninsa shugaban kungiyar Lauyoyi, Mounkaila Yaye, yace Imani da matsayin shari’a a tafiyar kasar dimokaradiyya ta kowanne fanni, yasa kungiyar lauyoyi zakulo wannan maudu’i da ake ganinsa tamkar gugar zana ne ga masu tafiyar da al’amura a jamhuriyar dimokaradiyar Nijar.

Gwamnatin Nijar ta ce ba zata yi ‘kasa a gwiwa ba wajen ‘daukan matakan inganta fannin shari’a, kasancewar dimokaradiyya ba zata girku ba muddin ba a baiwa fannin shari’a cikakken ‘yancin gudanar da aikin ta ba.

Taron dai ya samu halartar tawagar lauyoyi daga kasashe takwas mambobin kungiyar UMOA, baya ga wakilan lauyoyin Faransa da na wasu kasashe renon Faransa.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG