Accessibility links

Kungiyar Likitocin kasa da kasa ta gudanar da aikin rigakafi a kasar Guinea


Wata mata mai fama da cutar kwalara

Kungiyar likitocin kasa da kasa Doctors Without Borders, ta yiwa sama da mutane dubu dari rigakafin cutar kwalara a kasar Guinea.

Kungiyar likitocin kasa da kasa Doctors Without Borders, ta yiwa sama da mutane dubu dari rigakafin cutar kwalara a kasar Guinea.

Kungiyar tace, wannan ne karon farko da ta gudanar da irin wannan shirin a nahiyar Afrika, inda aka yiwa mutane allurar rigakafi daidai lokacin da aka sami barkewar cutar kwalara.

Kungiyar tare da hadin guiwar ma’aikatan jinya a kasar, ta kamala kamfen rigakafin cutar kwalara inda ta digawa mutane dubu 117 maganin rigakafin a baki a yankin Boffa na kasar Guinea, dake tazarar kilomita 150 da Conakry babban birnin kasar.

Kungiyar ta kai agaji ne sakamakon barkewar cutar da aka samu a yankin, daukar wannan matakin a daidai wannan lokacin inji darektan shirin a Geneva, Francois Vehoustaeten, ba kawai zai taimaka wajen jinyar wadanda suka kamu da cutar kadai ba, amma zai kuma zama rigakafi ga wadanda ke cikin hatsarin kamuwa da cutar.

Kasar Guinea da sauran kasashe a yammacin Afrika suna yawan samun barkewar cutar kwalara wadda ake samu ta wajen cin gurbataccen abinci ko ruwan sha.

XS
SM
MD
LG