Accessibility links

A Makonnan ne Kungiyar Malaman Jami'o'i Zata Janye Yajin Aikin Take Yi?

  • Aliyu Imam

Dalibhan jami'o'i da ma'aikata suke zanga zanag a Legas sakamakon yajin aikin malaman jami'o'in kasar.

Shugaban kungiyar malaman jami'o'i Dr. Nasir Isa Fagge yace kungiyar zata zauna domin shawarwarin watakil su koma bakin aiki.

A cikin wannan makon ne ake sa ran malama jami'o'in Najeriya wadanda suka shiga yajin aiki tun ranar daya ga watan Yulin bana, zasu janye yajin aikin, bayanda suka cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya cikin makon jiya.

Tuni aka ce gwamnatin tarayya ta cika daya daga cikin sharuddan da kungiyar ta gindaya na ganin gwamnatin tarayya ta kai kudade naira Milyan dubu metan (200 billion) zuwa ga babban Bankin Najeriya, da nufin a raba su ga jami'o'in kasar baki daya.

A hira da yayin da wakilin Sashen Hausa ta woyar tarho shugaban kungiyar malaman jami'o'in Dr. Nasir Isa Fagge, yace kungiyar zata zauna da wakilanta baki daya domin ta gaya musu abunda aka cimma da gwamnati.

Da Nasiru ya tambayeshi shin ko dalibai su fara mrunar zasu koma aji cikin makonnan sai yace, a dan basu lokaci su tattauna saboda dalilai da bayar kamar haka.

XS
SM
MD
LG