Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Masana Doka Ta Shirya Taron Duba Tsarin Mulkin Shugaba Mai Ruwa Biyu


Dr Dagra Mamadou na kungiyar masana doka da suka shirya taron da ya kunshi kasashen Nijar da Benin da Senegal

Kungiyar masana doka da hadin gwuiwar fanni koyas da ilimin shari'a da tattalin arziki na jami'o'in Yamai da Tawa suka shirya taron.

Manufar taron shi ne duba alfanu ko rashin alfanun tsarin mulkin shugaban kasa mai ruwa biyu, shirin da ya kafa shugaban kasa da kuma na firayim minista a kumshe inda shugaban kasa ne ke bashi izinin kafa gwamnati.

Irin wannan shirin wasu na ganinsa tamkar wata igiyar dake dabaibaye alamuran gudanar da harkokin mulki a kasashen da dimokradiya dinsu bata nuna ba. Shirin kan kawo takunsaka sakanin shugaba da firayim minista.

Dr Ahmadou yace sun shirya taron ne domin su tattauna akan irin yadda aka tsara gwamnatin Nijar mai shugaban kasa da firayim minista. Yaya gwamnatin ke tafiya kuma menene matsalolin da suke fuskanta, musamman tsakanin shugaban kasa da firayim minista.

Manyan malaman fanni shari'a a jami'o'in kasashen Nijar da Benin da Senegal ne suka bada kasidu.

Dr Dagra Mamadou na jami'ar Yamai yayi karin bayani dangane da abun da taron ke tattaunawa. Yace idan aka yi shugaban kasa mai cikakken iko, wato yana da rinjaye a majalisar kasa babu matsala. Idan kuma hakan bai samu ba to za'a dinga rikici musamman a kasashen da dimokradiya dinsu jaririya ce

Kungiyoyin fararen hula da aka gayyato sun fara nuna shakku a game da manufar wannan haduwa ta taron bisa ga alakari da irin dangantakar dake tsakanin wasu a taron da gwamnatin Nijar. Shakkun ma sun karfafa ne saboda taron ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Nijar ke kokarin yiwa kundun tsarin kasar kwaskwarima.

Malam Lawali Adamu shugaban wata kungiya yace ana kokarin a juya ne a fito daga mulkin mai ruwa biyu zuwa guda saboda wadanda aka gayyato daga kasashen waje sun fito ne daga inda ake kokarin zaben raba gaddama akan kawar da ruwa biyu zuwa daya, wato shugaban kasa mai cikakken iko. Mutanen da suka sa kasarsu cikin rudani su ne kuma suka kasance wurin taron.

Baicin haka, kungiyar da ta shirya taron kungiya ce dake kusa da gwamnati. Mambobinta na cikin babban kwamiti na kotun tsarin mulkin kasa.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG