Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Mayakan Hamas Ta Rusa Majalisar Gudanarwarta


Wasu Daga Cikin Manyan Jami'an Kungiyar Hamas da Fatah Bayan Sasanta Tsakaninsu.

Kungiyar Fatah da Hamas sun hade kan shugabancin Zirin Gaza

Kungiyar mayakan Hamas dake iko a zirin Gaza ta dauki mataki yau lahadi na kawo karshen takun saka da sabanin siyasa da kungiyar Fatah ta shugaban yankin Palasdinawa Mahmoud Abbas, inda ta amince da rusa majalisar gudanarwarta, da gudanar da babban zabe.

Yayinda tattalin arzikin zirin Gaza ya ruguje, samun wutar lantarki kuma ya koma sa’oi hudu a wuni, kungiyar Hamas tace zata kyale gwamnatin hadin kai ta shugaba Abbas ta yi jaroganci ba tare da bata lokaci ba. An kafa gwamnatin hadin gwiwar ne shekaru uku da suka shige, amma bata sami ikon gudanar da mulki ba a Zirin Gaza sai yanzu.

An sami wannan ci gaban ne bayan zaman tattaunawa dabam dabam da wakilan kungiyoyiyin Hamas da Fatah suka yi da jami’an leken asirin kasar Misira a birnin alkahira.

Mahmoud Aloul, wani jami’n Fatah ya yi na’am da yarjejeniyar, sai dai ya shaidawa wata tashar radiyon Palesdinawa cewa, “muna so mu gani a kasa kafin mu dauki mataki na gaba”.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG