Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Nakasassu Ta Damagaram Ta Koka Kan Nuna Musu Wariya


Tambarin Jamhuriyar Nijar

Babbar kungiyar nakasassu ta Damagaram ta koka da yadda ake nuna musu wariya game da kayayakin da suke kerawa, duk da kiraye-kirayen da ake musu na su daina bara su rungumi sana’a.

A cewar ma’ajin kungiyar nakasassun, Sa’idu Jibo, dukkan su maza da mata sun daina bara sun rungumi sana’o’i amma babu ci gaba domin ba a sayan kayan na su, ana kyamar su.

Kungiyar nakassun dai ta bude wata cibiya da ta hada da guraren koyar da aikin hannu irin su ‘Dinki da Walda da aikin Kafinta da grayan inji da kera kekunan guragu da kuma kera kofofi da dai sauransu.

Yanzu haka dai babbar matsalar nakasassun itace rashin sayen kayayyakin na su, inda har ta kai suna tambayar kansu cewa ko ana nuna musu kyama ne, ganin yadda suke kera kayyayyaki masu inganci.

Domin karin bayani saurari cikakkiyar hirar Tamar Abari da Sa’idu Jibo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG