Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan al-Shabab Sun Kaiwa Jami'an Tsaron Somaliya Hari


A kalla sojojin Somaliya biyu da ‘yan bindiga 12 ne aka kashe jiya Juma’a, lokacin da mayakan kungiyar al-Shabab suka kaiwa jerin gwanon motocin jami’an tsaro hari a yankin tsakiyar kasar Somaliya, a cewar wani babban jami’in yankin.

‘Yan bindigar sun kai harin kwantan bauna ga jerin gwanon motocin jami’an tsaro dake ‘dauke da gwamnan Hiran, Ali Jeyte Osman, da kuma wasu manyan jami’an soja, kusa da ‘kauyen Hees, dake da tazarar kilomita 80 arewa maso yammacin birnin Beledweyn.

Da yake magana da sashen Somaliyanci na Muryar Amurka, kwamandan sojojin tarayya a yankin, Janal Ahmed Mohammed Tredishe, ya ce “Mun kashe mayakansu 12, kuma mun rasa sojojinmu biyu.

Ya ce gwamna da sauran jami’an soji dake wannan tafiya babu abin da ya samesu kuma sun ci gaba da tafiyarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG