Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar NLC Ta Yi Tattaki A Kaduna Domin Zanga-Zangar Ma'aikatan Da Aka Kora


NLC KD

Duk da barazanar kama mambobinta a jihar Kaduna, kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta fara zanga-zangar gargadi ga gwamnatin jihar game da korar ma’aikatan da ta yi.

Zanga-zangar da ta hada da yajin aiki na kwanaki biyar dai ta yi sanadin rufe gidajen mai, asibitoci, bankuna, makarantun gwamnati da sauran cibiyoyin gudanarwa da ke fadin jahar.

Kwamared Ayuba Wabba shine Shugaban kungiyar na kasa kuma shi ya yi jawabi kan dalilin daukan wannan mataki.

NLC KD
NLC KD

Ya ce ba'a taba yajin aikin da hatta jiragen sama da na kasa basa shiga Kaduna ba. Kuma in aka tuna baya an kori mutum dubu biyar wanda har yanzu ba'a biya su ba.

Karin bayani akan: Ayuba Wabba, Kaduna, NLC, Nigeria, da Najeriya.

Shuwagabannin Kungiyar kwadago na kasa da dama sun halarci wannan zanga-zangar a Kaduna kuma sun ce dama alkawari su ka yiwa juna, kuma sun cika alkawarun da suka dauka domin nuna bacin ransu.

Har kungiyar kwadagon ta gama wannan zanga-zangar dai gwamnati ba ce komai ba ko da yake kafin fara wannan zanga-zangar kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jahar Kaduna, Malam Jafaru Sani ya gargadi 'ya'yan ungiyar kwadagon baki daya game da wannan yunkuri.

Duk da fargaban tashin hankali yamutsin da gwamnatin jahar Kaduna ta bayar dai, taron zanga-zangar ya ta shi ba tare da wata bayananniyar matsala ba.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG