Accessibility links

Kungiyar Radun Yaki da Cin Hanci da Rashawa Zata Kai Gwamnatin Kano Kotu


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso
Wata kungiya dake radun yaki da cin hanci da rashawa dake da ofishi a Kano ta yi barazanar kai gwamnatin jihar Kano kotu kan zaben kananan hukumomi.

Kungiyar tace daga bayyanan dake hannunta ta gano cewa an bayarda kwangilar kayan zaben ta hannun ma'aikatar kananan hukumomi ta jihar lamarin da kungiyar ta ce ya saba ma dokoki da kaidojin gudanar da zaben kananan hukumomi musamman idan an yi la'akari da dokar da ta kafa hukumar zabe mai zamankanta.

Shugaban kungiyar Muibi Magaji yace an cire kudi nera miliyan goma sha bakwai da dubu dari daga kowace karamar hukuma. Kwanigilar sayen kayan zaben sai kuma aka baiwa ma'aikatar kananan hukumomi. Idan haka ne wato ma'aikatar kananan hukumomi ke yin zaben ba hukumar zabe mai zamankanta ba ta jihar. Wannan komacal bata dace ba.

Dokar da ta kafa hukumar zabe tace idan hukumar na aikinta kada ta zama karkashin kulawar ko jagorancin kowane mutum ko hukuma. Dokar ita ce ta bata 'yancin zamankanta. Dokar tana son kada ta kowa ya juya mata akalar aikinta. Sabili da haka shugaba Magaji yace ba zasu bari ba. Zasu yi abun da ya dace, wato kai gwamnatin jihar kotu inda za'a warware maganar da kuma tantancewa.

Amma Alhaji Ismail Idris Garba kwamishanan yada labarai na hukumar zaben mai zamankanta yace kowace kungiya na iya samun labari daidai da wanda ba daidai ba sabili da haka ba'a inganta labari sai an tabbatar da sahihancinsa. Yace abun da kungiyar ta samu ba sahihin labari ba ne. Yace hukumarsa, wato hukumar zabe ita ta bashi takardar kwangila ya je ya kawo masu kayan. Yace kuma kafin a bayarda kwangilar sai da shugaban hukumar da dan kwangilar suka je gaban babban mai shari'ar jihar suka sa hannu kan yarjejeniyar kwangilar. Alhaji Garba yace abun da ya kaisu kotu tsakaninsu ne da dan kwangila. Babu ruwan ma'aikatar kananan hukumomi.

Ga rahoton Mahmud Kwari
XS
SM
MD
LG