Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Sabunta Muradun Kasa Bata Gamsu da Matakan Farfado da Nera Ba


Kungiyar Sabunta Muradun Kasa ko NRG

A cigaba da neman mafita daga tabarbarewar tattalin arzikin kasa, Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya ta amince da wani sabon tsari na sake karfafa Nera akan kudaden waje

Gwamnan Babban Bankin Najeria Godwin Emefiele shi ya dauki matakin inda ya sako wasu kudade dallar Amurka miliyan dari biyar da talatin a makon jiya kuma yanzu ma ya sake sako wasu miliyan dari da tamanin.

Wannan kokarin fitar da kasar daga koma bayan tattalin arziki da ta shiga tun daga shekarar 2014 da karfin darajar Nera ya ragu yayinda ta fadi har ana sayar da dallar Amurka daya akan Nera 550.

To saidai matakin bai gamsar da 'yan kungiyar Sabunta Muradun Kasa, ko National Rebirth Group ba.

A cewar sakataren watsa labarai na kungiyar NRG Isa Tijjani bincikensu ya nuna cewa kudurorin gwamnati basa tafiya daidai da halin da 'yan kasa ke ciki. Yace kudure-kuduren gwamnatin yanzu suka janyo halin da kasar ke ciki saboda abubuwa da dama da gwamnatin tayi da ba daidai ba. Inji Isa Tijjani kusan kashi saba'in na mutanen kasar basa iya cin abinci sau biyu a rana guda saboda tsananin talauci.

Amma daya daga cikin dattawan jam'iyyar APC mai mulki daga jihar Jigawa Husseini Dariko yace kyawawan manufofin gwamnati na tafiya saidai rashin hakuri irin na mutane. Yace har gobe talakawa suna bayan Buhari, amma wadanda suka ce suna tare da shugaban kasa kadan ne suke tare dashi da gaskiya. Wasunsu suna son suyi barna ne domin su shafawa shugaban kasa kashin kaza. Kamata yayi a yi tankade da rairaya domin a cigaba, inji Husseini.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG