Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Afrika tayi Allah wadai da rikici a kasashen Sudan


Wadansu sababin kuratan sojojin kungiyarSudan People's Liberation Army (SPLA)

Kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika ta bi sawun Amurka wajen yin Allah wadai da tankiyar dake kara zafi, tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

Kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika ta bi sawun Amurka wajen yin Allah wadai da tankiyar dake kara zafi, tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, da a wannan makon ta hada da kai hare hare ta sararin sama da kuma kasa.

A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Talata da yamma, shugaban kungiyar Jean Ping ya yi kira ga bangarorin biyu su mutunta yarjejeniyoyin da aka rabbatawa hannu kwanan nan, ya kuma bayyana cewa, tilas ne a warware rashin jituwa ta hanyar lumana. Ya bayyana takaicin ganin lamarin ya auku ana shirin tattaunawa tsakanin shugaban Sudan da takwaranshi na Sudan ta Kudu, dangane da rikicin kan iyaka da kuma albarkatun kasa.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yace ya janye taron kolin da ake shirin gudanarwa ranar uku ga watan Afrilu da shugaban kasar Sudan ta Kudu salva Kirr ne, sabili a tashin hankalin.

Cibiyar tsugunar da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa dangane da kula da lafiyar kimanin ‘yan gudun hijira dubu goma sha shida daga Sudan da suka kauracewa matsugunansu dake tsaunukan Nuba zuwa matsugunan Yida dake Sudan da Kudu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG