Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Tallafawa Kasar Nijar Da Makudan Kudade


Kudaden Yiro
Kudaden Yiro

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta tallafawa kasar jamhuriyar Nijar da kudi sama da Yiro Miliyan 107 domin samar da mulki na gari da yaki da talauci a kasar.

A wata sanarwa da ofishin jakadancin kungiyar Tarayyar Turai dake Nijar ya fitar ya bayyana cewa kungiyar EU ta tallafawa Nijar da kudi sama da Yiro Miliyan 107 da Dubu 500. Sanarwar tace tuni aka zuba wannan kudade a asusun baitulmalin kasar Nijar.

Kungiyar EU ta tallafa da wannan kudi ne a matsayin gudunmawar da ta shafi tsarin kasafin kasar Nijar na shekarar 2016. Yanzu haka dai shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou na kammala wata ziyara a birnin Brussels a yau Juma’a.

Tuni dai kungiyar EU ta fayyace tsarin da za a bi wajen amfani da wadannan kudade, ayyukan da za a gudanar sun hada da samar da abinci da ayyukan bunkasa noma, sai kuma tanadin abinci domin taimakawa jama’a lokacin rani, da kuma inganta ilimin yara da inganta sha’anin Shari’a da tsaron gida.

Tallafin dai ya biyo bayan tattaunawar da akayi tsakanin bangarorin gwamnati da Tarayyar Turai, kuma yana cikin wani bangare na tsarin kafin shekara ta 2016.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Mumuni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

XS
SM
MD
LG