Accessibility links

Kungiyar Tijjaniya Tayi Taron Addu’oi A Najeriya

  • Grace Alheri Abdu

Musulmi Suna Sallah

Kungiyar Tijjaniya ta yi kira ga shugabannin addinai a ko'ina suyi addu'oi domin samun zaman lafiya mai dorewa a Najeriya

Kungiyar Tijjaniya ta gudanar da wani taron gangami na kasa da kasa a Najeriya a Najeriya domin addu’a ta musamman da nufin ganin an sami zaman lafiya a Najeriya.

Kungiyar ta da hada kan membobin daga kasashen Afrika dabam dabam da kuma samun wakilci daga Turai, tayi kira ga shugabannin addinai a ko’ina suyi addu’oi domin neman zaman lafiya mai dorewa a Najeriya.

Wakilai daga kasar Kamaru sun bayyana cewa, ci gaban yankinsu ya dogara ne ga zaman lafiya a Najeriya sabili da haka suka jadada bukatar samun zaman lafiya a kasar.

Wakilinmu Nasiru Adamu el-Hikaya ya ruwaito cewa, kungiyar zata gudanar da taron mauludi a Dutse cikin karshen mako.
XS
SM
MD
LG